Aboki na gari shine wanda ko yaushe yana tare dakai
Mohammed Albarno.
Sau da yawa mutane na cin karo da abokanan banza, wanda hakan shi ke jawo ma mutum matsaloli da yawa. Kamar matsalar rayuwa, matsalar samun taymako, ko mafita a wani yanayi da ake bukatar mafita.
Rashin dacen aboki, kan sa mutum zama wani iri, domin mutum Addinin abokin sa yake bi bana iyaye ba. Ma'ana, mai abokin sa yake yi, me yake so, me baya so, wane irin kaya yake so. Duk wani abinda abokin sa yake so shima yana so. Hatta abinci ko tafiya ko salo, mutum duk na abokin shi yake kwaykwaya.
Aboki na gari nada wahala, domin mutum zai iya samun abokai masu yawa, amman akasarin su mahasssada ne, kuma makiyan boye ne.
Aliyu Zakar Ya'u (Asadullah/Alincy)
Wasu abokai suna son zama kai ne saboda wani matsayi naka. Watakila kana da kudi, ko ilimi da ake yabon ka dashi. Watakila kana aikata wani abu da ke haska tauraron ka, wannan ne yake sawa wasu su nemi ka, har su zama abokin ka. Amman da zarar ka rasa wayan nan abubuwan, to dukan su zasu kwaye maka. Wasu abokan har neman kashe ka zasuyi, wasu neman jefa ka a damuwa zasuyi.
Duk abokin da kaga yana Allah Allah kayi laifi yayi magana akai, to ba abokin kwarai bane. Aboki na gari shine wanda baya son ya ga kayi laifi, kuma in kayi din ma baya son wani yaji, shi kadai zai maka nasiha ba tare da wani ya sani ba. Wannan shine abota ta gari. Kuma duk wanda yana da irin wannan abokin, rike shi hannu biyu kar kayi wasa dashi.
Aliyu Adamu Yaro (Ashuur/Abokin Aljanna)
Har Ila yau, wasu abokai suna tare dakai ne na dan wani lokaci dan su cimma wani burin su. Da zarar wannan burin ya cika to shikenan zaman ku tazo karshe. Irin wannan abokai kar kayi saurin fada musu sirrin ka, domin in har ka gaya musu to ya zama ba sirri ba.
Shin kana da aboki wanda ya damu da damuwar ka ? Wanda ko yaushe yana tare dakai, baya kiyamar ka saboda baka da shi, kuma baya Gulman ka saboda rashi. Wanda ya kasance yana da aboki mai matukar nuna damuwar sa akan ka, to dan Allah kar ka rabu dashi.
Muhammad Isa Biu (Babs)
Da Abokin kwarai ake samun nace na gari. Allah idan har baka da aboki na gari zaiyi wuya ka samu mace ta gari. Domin kana samun mace koda kuwa ja'irace, tsabar farin ciki abokin ka zai ce tayi. Sai bayan anyi aure ne zaka fahimci yaren da na shina.
Me zakayi da Abokin da yana son ka dan kudin ka? Da zarar ka talauce ya guje ka. Irin wadannan abokai, sune wayanda bayan idon ka suna da.
Naseer Abdullahi (Alhajin Matasa)
A'uzubillah, aboki da shine zai maka sharri dan zubar da muncin ka. Me anfanin zama da irin wannan abokai.?
Sannan Alhamdulillah, akwai abokai da, kana shiga cikin damuwa, kana neman mafita, kafin ka gaya musu tuni har sun san me yake damun ka, sannan su taymaka maka da iya abinda suke dashi.
Ammar Muhammad Yola
Tbutulci ne ka manta da abokin da ya nuna maka tausayi a lokacin da baka dashi. Kasan in kayi kyauta ga abokin ka watarana zai dawo kan ka? Kasan da zarar ka taymaki abokin ka a lokacin da baya da shi ba zai taba mantawa dakai ba.
Ya Allah ka bamu abokai na gari. Basu son mu Dan Allah, Wanda ba zasu cutar damu ba. Allah ka san su, ka nuna mana su ko a ina suke. Allah kasa muma mu so aboki na gari, mu rike shi hannu biyu.
Mohammed Umar Albarno