Rashin Uba rashin gata
Ko wane Da, yana alfahari da Uban sa Amman ban da ni...!
Chikakken mutunci da yanci ga mutum shine wanda ya taso tare da iyayen sa. Iyeye suke bawa mutum gata ta ko wane hali, wanda koda ace basu da komai ba zasu rasa nayi masa komai ba.
Musamman ga wanda yayi rayuwa tare da Uban sa, sai kuma mama.
Uba shine wanda yake jagorantan dan sa zuwa ga aikata aiki mai kyau. Koda Uban ya kasance mutum ne mara tarbiya, to ba zai taba yarda rarbiyan Dan sa ya lalace ba.
Koda uba ba shi da abinda zai baka, ba zai barka hakanan ba, ba tare da ya sanya ka zuwa ga hanya mai kyau ba. Zai baka shawara ko umarnin yin wani abu da zai zama maka garkuwa a rayuwa, sannan zai kula maka da lokacin da ya kamata ka aikata wani abu. Kamar karatu, Kasuwanci, Aure, ko samun gida.
Wayanan gatan duk sune na rasa su, sakamakon rashin uba. Naso ace na taso tare da uba na, wanda da a halin yanzu na wuce level da nake ciki, ko wulakancin daga wajen da ma bai kamata ba.
Naso ace na taso da uba na, wanda zai tsawata min, tare da cewa kayi kaza. Ko ya dauke ni muje wani wuri dan ya bude min ido na, ko ya ciyar dani abinda ban taba ci ba.
Naso ace na taso da ubana, wanda zanje wajen shi nayi masa shawagaba, nace baba ina bukatar kaza. Baban kudin makaranta, baba kudin kaya, baba kudin mota, baba kudin dakin makaranta, baba kudin kayan sallah.
Naso ace na taso da babana, wanda idan ya ganni da Abokan banza ya min bulala. Ko yace wannan aboki bana kwarai bane. Ko ya zaba min aboki na gari.
Naso ace na taso da babana wanda zan ji zafin bulalan shi, nace masa baba I love you.
Naso ace na taso babana, wanda idan wani ya taba ni zai karbo min haqqi na. Idana aka cuce ni ya faranta min, idan aka zage ni ya lallashe ni.
Naso ace na taso baba na, wanda zaice wane je kayi aure, ko ga kudi ka kai sadaki, ga gida, ga mota.
Naso na taso da babana wanda ba zai taba yarda na kwana da yunwa ba. Wanda zaije wane ga kudin abinci, wane ga kaci abinci kuwa? Wane me yasa baka ci abinci ba, wane me ya taba ka, wane wane hali ka shiha.
Naso ace baba yana tare dani, da kai masa karat wayanda suka bata min rai. Da na kai masa kukan wayanda suka taba ni. Da na gaya masa sunan matar da zan aura a kunne dan yasa mana albarka.
Naso ace, babana yana raye, ya sanya hannun sa a kafada na, yace min dana nace masa babana.
Naso ace ubana yana nan, na kira sa baba ba tare da wani yamin gorin uba ba.
Naso ace ina tare da baba, naci abinci tare dashi ba tare da wani yaji cewa ina gama masa abincin gidan uban sa ba.
Naso ace na taso tare da baba, wanda wani bai isa ya hanani shiga gidan sa ba, ko ina cin abincin gidan ran shi na bace wa.
Naso ace na taso da shi wanda wani ba zaice min da shayi da bredi aka ciyar dani ba.
Naso ace ina tare dashi, da ban cika shiga doguwar tunani wanda har yake sani rama sossai ba.
Da baba yana nan da ban rasa wadanan gata ba, da ya na nan da baki umma bai cika rufuwa ba. Da yana nan da ina da kanne masu sharen hawaye. Da yana nan da nayi Alfahari dashi.
To baya nan, babu shi bare nayi Alfahari dashi. Ban zauna dashi ba. Shekara daya mukayi dashi. Ya soni, yayi murna tun daga ranar da aka haife ni har zuwa rufewar idon sa. Tsabar murna da zuwa na duniya, a ranar da aka haife ni rago ya yanka, sannan ranar da akayi suna na raguna aka yanka. Yaso ni, yayi Alfahari dani, to ni tayaya zanyi Alfahari dashi. Ina so nayi Alfahari dashi amman tayaya? Nayi ta masa addu'a da kuka, ko zaiji ni amman banji komai ba. Na tana hasashen ko zai min magana banji ba. Ina shirin naji yamin tsawa amman banji ba.
Wayyo Allah, mutuwa baki min Adalci ba. Kin tafi min da abin soyuwa amman kin barni a duniya tarbiya ta na lalacewa babu mai gyarawa. Idan na zama mai aikata sabo, rashin mai min fada ne yasa. Idan na zama wawa rashin mai wayar dani ne. Idan na zama jahili rashin mai min jagora ne. Idan na zama rayuwa ta sai a hankali rashi uba ne.
A wannan wata, bayan sallar azumi da kwana 5 Allah ya dauki ran mahaifi na. Allah ka jikan shi, ka gafarta masa, ka daukaka darajar sa. Ka sa ya huta, ka sadani dashi a kiyama. Kasa na samu gatar shi a lahira. Kasani a damshin babana.
Allah kasa na gana dashi koda kafin na mutu ne. Inkuma bayan na mutu ne Allah kasa ya zamana a cikin masu tarba na.
Baban mu ina nan a raye, na kosa mu hadu, rayuwa babu dadi saboda kai. Danka na wahala, bashi da wani gata, saboda babu kai. Da yanzu kananan nasan da na gama Degree nawa na 2. Ina karatu ne dan na faranta maka rai, nasan da kana raye hakan saka so. Duk ranar da naga rubutun da kayi da hannun ka sai naji na kara samun natsuwa.
Masoyana, ku yi ma babana addu'a, Allah jikan shi. Yau shekaru sama da 20 kenan da Allah yayi masa cikawa.
Allah ka jikan Malam Umar, mahaifi ga ni Muhamma Auwal. Sunan da kasa min kenan, kuma har yanzu ina amsawa.
Ameen ya Allah!