Yau ASUU ke cika kwana 100 da fara yajin aiki
Yajin aiki da aka soma tin watan 2, zuwa yau ba tare da komawa makaranta ba, yau kwana dari kenan, dalibai na makale a gida.
Yajin aikin, yaki ci yaki daidaituwa bisa bukata da kungiyar Malaman jami'a ke nema, wanda su kuma Gwamnati har zuwa yanzu ta kasa yi musu komai.
A farkon wannan watan ne, Gwamnatin Nigeria, ta bukaci tare da rikon kungiyar ta Malaman jami'a da su janye yajin aiki, su kira dalibai su koma karatu. Sai dai kungiyar har zuwa yanzu suka ce ba zasu daina yajin aikin ba har sai an biya musu bukatun su.
Gwamnati, tayi musu barazanar cewa, Babu aiki Babu kudin salari da ake biyan su, amman duk da wannan barazanar har zuwa yanzu yajin aikin bai kawo karshe ba. Wata majiya na nuna cewa yajin aikin na iya kaiwa zuwa karshen shekaran nan indai Gwamnati bata biyawa ASUU bukatan su ba.