Shekaru 10 da rashin ka Sarkin Gwoza Shehu Mustapha Idriss Timta
Baba Ina mai gaya maka.

Tun da ka tafi ka bar mu a haka.
Babu cigaba kuma babu haɓaka.
Sun kashe Sir Isa Dan uwan ka
Sun rakarkata maka garin ka
Sun keta haddin muradun ka
Sun kona duk wani makarantun ka
Sun daina daraja iyalan gidan ka
Kulluma kunci harda kuka
An daina yin noma a garin ka
Mutanen ka sun koma maroka
An maida su yawo kamar hauka
Zuciya ta rube kamar tauka
Babu wani babba da zai tuna ka
Magana nake kamar waka
Mai tunani kadai zai san haka
Gaskia nake amman fahimtar ka
Roko nake, ka tsaya a haka
Me suke da shi da zan roka
Bayan ni dasu akwai doka
Kar ka tsaya bata lokacin ka
Gaskia ɗaci take ina gaya maka
Me suke da shi da zasu baka
Bayan kai dasu kun wuce haka
Sun dade suna satar kudin ka
Sun kasa yi maka abin cigaban ka
Babu wakilci da zai nuna ka
Kunya zaka ji idan anyi haka
Da su nake ƴan siyar ka
Ka rike su kamar Allahn ka
Tunani kake su daukaka
Bayan ma daga kai suke samun daukaka
Babu kai babu su ka shaida haka
Da ka, ka, ka, nake sauke haka
Magana nake saɓanin fahimtar ka
In ka gane ya ishe ka haka
In kuma ka kiya ku shaida haka
Allah yayi rahama ya kuma jikan ka
Gaskia daya ce, mun rasa ka
Tags:
Gwosa Post