​Abin da Hakuri Bai Baka ba tashin Hankali ba zai baka ba



Mohammed Albarno


Wani yanayi da yake ciwa matasa masu tasowa tuwo a kwarya shine Hakuri. Ma'ana rashin yin a hakuri tare da maida hankali akan abin da mutum ya sa gaba. Galiban matasa na rasa cimma burin su a rayuwa sakamakon rashin samar da wasu abu da zai taymaka musu a yayin tafiyar.


Tabbas matashi a lokacin da yake tasowa, zai rika jin wani iri, musamman ma ace bai samu biyan bukata na wani abu ba, a lokacin da yake bidar abin. Misali irin su kudin kashe wa, ko kudin sayan wani abu na more rayuwa. Kayan sawa, ko wayan zamani, ko kuma mallakar wani abu da wani daga cikin abokanan sa ya mallaka.


A irin wannan lokaci da matashi ke bukatar abu, da zarar kace masa yayi hakuri, komai lokaci ne, to maganar gaskia zuciya ba zata yi saurin dauka ba, dole zai rika daukan mai ce masa yayi hakuri din tamkar makiyin sa ne da baya son cigaban sa.


Har ila yau, Hakuri, abune mai kayu da yakamata ko wanne dan madam mumini ya kasance yana dashi. Haka ne ma Allah yace, yana tare da mai hakuri.


Tabbas maganar gaskia, hakuri zamu iya cewa abune mai sauki, amman saidai babu abinda yafi konawa mutum rai kamar a ce masa yayi hakuri. Kamar yadda na fada a sama, wani lokaci wanda aka ce masa yayi hakuri, kallon makiyi yake ma wanda ya gaya masa kalamar.


Wani lokaci, idan aka ce maka kayi hakuri, hawaye kawai zai rika zuba maka a ido. Babu ma kamar a ce wanda ya baka hakuri din wani mutum ne babba daga gare ka.


Na'am, hakuri nada kona rai, tare da sa mutum takaici. Yaji kamar ace shi dinnan, wane ya bata masa rai amman ace yayi hakuri? Bayan yana da daman da zai iya ramawa. Watakila matar sa ne, ko iyayen sa, ko kuma 'ya'yan sa ne, ko Yan uwan sa. 


Babu abinda yafi kona rai a maganar hakuri kamar ace, abu ne da bai fi karfin ka ba, sannan ace kayi hakuri, wannan yafi ko wanne bari game da hakuri zafi.


Amman gaba daya wannan lamarin, Idan mukayi nazari, daga karshe zamu fahimci cewa abinda hakuri bai bayar ba, rashin sa ba zai taba badawa ba. Yan uwa na, mu daure, mu ci gaba da hakuri a kowanne lamaran mu. Mai hakuri yana tare da riba, mai hakuri yana tare da sa'a, kuma mai hakuri ne kadai ke iya dafa dutse.


Allah ka yayyafa ruwan sanyi ga zukatan mu yayin da wuta ke tafasa su. Allah zuciyan hakuri zuciyan Gol ne, ka bamu shi. Allah duk wani abinda zai kawo tashin hankali bisa rashin hakuri Allah ka rabamu da shi. Allahumma Ameen