Tsadar rayuwa: Ɗalibai na kaurace ma karatun jami'a a Nijeriya
Tsadar rayuwa: Ɗalibai na kaurace ma karatun jami'a a Nijeriya
Daga Muhammad Albarno
A wata sabuwar yanayi da kasar Nijeriya ke ciki, wanda yasa ƴan kasa da dama ke fuskantar matsala ya rayuwa, jami'o'i a Nijeriya na fuskantar barazana da yasa dalibai na kaurace mata. Hakan yasa, matasa da suka kammala karatun su na sakandare, mai makon zuwa jami'a dan cigaba da karatu, amman lamarin ya chanza ba kamar yadda yake a baya ba.
Jami'a, makaranta ce da ke karɓan yara da suka zana jarabawar JAMB, dan gudanar da karatun su ta didiri. A baya yawan ɗalibai da suke samun damar shiga jami'a na da yawa, wanda ya zarce yawan ɗalibai da suka nemi damar shiga jami'a ta wannan shekarar.
Jami'a, makaranta ce da ke karɓan yara da suka zana jarabawar JAMB, dan gudanar da karatun su ta didiri. A baya yawan ɗalibai da suke samun damar shiga jami'a na da yawa, wanda ya zarce yawan ɗalibai da suka nemi damar shiga jami'a ta wannan shekarar.
Jami'ar Maiduguri, na daga cikin manyan jami'o'i da suka fi kowa daukan dalibai. Alkalamin ya nuna, a shekara ta 2020, 2022, jami'ar ita ta biyu a wajen daukan ɗalibai masu yawa. daga jami'a ta online NOUN, sai jami'ar Maiduguri, inda a baya tana daukar ɗalibai sama da 15,000 ko wane shekara, saɓanin wannnan shekara da yawan ɗalibai da aka dauka bana ba kai rabin yawan da ake samu a baya ba.
Wasu dipatment, kamar na; Motsa Jiki, da kuma malaman lafiya (Physical & Health Education, a baya suna daukan ɗalibai sama da 1,000 wanda wannan shekarar bai ma kai 400 ba. Haka zalika, Dipatment na English, a baya suna daukan ɗalibai 300, 200, amman wannan shekara ɗalibai 20 kawai kacan aka tabbatar da zaman su ɗalibai.
Daga cikin abubuwa da yasa hakan, akwai karin kuɗin makaranta da akayi a shekara ta 2022, wanda kusan ko wanne Faculty sun nasu kuɗi, daga dubu 28,000 zuwa 80,000, wasu ma kusan zuwa 120,000, 130,000. Masu zuwa karatu daga nesa da kuma cikin gida, sukayi tunanin cewa, lallai hakan babban jarabawa ce gare su. Wasu sun cire yaran su a makarantar, yayin da wasu kuma suka ji tsoro, a maimakon samar da yara 2 zuwa 3, zuwa jami'a, sai iyaye su rage.
Sai kuma batun, tashin kudin mai. Wannan ya shafi masu zuwa makarantar daga nesa. Musamman Yarabawa da Nyamurai daga kudancin Nijeriya. A baya kafin tashin kuɗin mai, su kan biya 15,000 zuwa 20,000 kachal zuwa Maiduguri daga garuruwan su. Wanda yanzu kuɗin ya ninninka daga wancan prise din zuwa dubu 60,000, 70,000. Ɗalibai daga Benuwe, Kogi, da Nasarawa kuma, a bayan 7,000 na iya biya musu kuɗin mota, yayin da yanzu kuma ya haura sama da 25,000. Wannan ma daga cikin yanayin da yasa ɗalibai suna kaurace ma karatu.
Har ila yau kayan abinci, da farko, a shekarun baya, ɗalibai na sayan Taliya 2,500, wanda yanzu yayi tsadar da ya kai 7,000. Kwanakin baya kam ma ya taba kaiwa 16,000, yayin da Indomi, ya kai 19,000 daga naira dubu 3,000. Kwanon shinkafa kuma daga 1,200 zuwa 4,000.
Abinda ake anfani da shi wajen dafa abinci, kamar rishon, da gas. Suma farashin su ya tashi. Kudin photo copy ya tashi daga Naira 5 zuwa Naira 50. Wanda a baya, abinda zakayi shi a Naira 50 yanzu ya zama naira 500, naira 100 kuka zuwa 1000. Komai farashin shi ya tashi da ninki goma.
Ɗalibai na son yin karatu, amman babu dama, yanayi yayi zafi, gaba daya gari babu dadi.
Musamman a Maiduguri, ga yanayin rashin wuta, rashin ruwa, da kuma zangon karatun ma ya tashi daga yadda aka sani a baya.
Hanyoyi da za abi a magance wannan matsalolin shine, gwamnati ta sake duba kan lamarin tattalin arzikin kasar, tare da inganta harkar ilimi. Idan har rayuwa zata koma kamar da, to na tabbata rayuwar dalibai zata inganta. Idan kuma haka za a cigaba, to lallai gwamnati tayi wani abu akai, kamar samar da motoci masu rahusa da zai rika dauko ɗalibai daga garuruwan su zuwa garin da suke karatu. Sannan a sake duba tare da rage kudin karatu. Me yake kawo tashin kayan abinci? Idan har shinkafa, masara, dawo taliya zasu cigaba da yin tsada, to zuwan da shekara 5 masu zuwa, za a nemi dalibai 2,000 a rasa su a jami'a.
Musamman ma yanzu, irin, gani da ake yi ma, idan ka wahala kayi karatu, babu tabbacin cewa zaka samu aiki. Ga tsadar rayuwa, ga kuma tsadar kudin makaranta. Wasu hatta kudin zana jarabawar JAMB ma basu da shi. Ina kuma ga kudin rijistar shiga makaranta. Kudin ɗakin da mutum zai zauna a ciki ma yayi tsada, komai yayi tsada. Sannan mafiya yawan ɗalibai kuma ƴaƴan manoma ne, iyayen su babu karfi, gonaki sun mutu, wasu wuraren ma rashin tsaro ya hana su noma.
Tags:
Press
