Tasirin Kallon Indiya Hausa a Nijeriya
Tasirin Kallon Indiyan Hausa a Nijeriya
Daga Muhammad Albarno
Finafinan India da ake fassara shi zuwa yaren Hausa, wanda yau kusan shekara 15 da bullar wanann salon, ya chanza rayuwan mutane musamman matasa da shekarun su bai hura 20 ba, tare koya musu darasi. Wannan darasin, wasu ƙalilan ne suke anfana da ɗabi'u na gari, yayinda mafiya yawan su sun karkata i zuwa rayuwar chaskale.
Indiyan Hausa, wanda ake fi sani da masuburbuɗa, ya fara bayyana ne tare da mamaye ƙasar Nijeriya da Nijer a shekara ta 2010, musamman a arewacin Nigeriya, yara sabon tashi, na maida hankalan su ɗari bisa ɗari wajen kallon su. Yayin da hakan yasa koda kuwa a makaranta ne, malamai ba zasu iya chanza rayuwar ɗalibai ba kamar yadda fassara ta Indiya Hausa zai yi.
Darussan da ke kunshe a cikin finafinan, sun haɗa ne da, rayuwa mai kyau, da kuma rayuwa mara kyau. Misali; yadda ake gudanar da mulki, da kuma irin zalunci ƴan sanda, har da yadda yan siyasa ke maguɗin zabe. Akwai jarumi wanda aka fi sani da (Star) kusan ko yaushe jarumi na fito wa a matsayin mutumin kirki kuma mai tausayi. Daliban jaruman, zaka same su, suna da abin a yaba musu, musamman bangaren soyayya, nagarta, duma ko wanne jarumi zaka ga Allah yayi masa kira mai kyau. A ɓangare guda kuma, akwai ƴan daba da uban daba, waton (Boss) da kuma bosawa. Su waƴan nan, rayuwar su na ta'allaka ne akan kisa, mugunta, giyaɗe, kalaman batsa, da kuma zalunci. Kusan duk wanda yake kallon fim din, kafin a gama, wasu iya kare wa kallon da hawaye a ido, wasu kuma da bugun zuciya, yayin da wasu kuma farin cikin. Masu ganin jarumi ya burge su, har sakan ma kansu sunan jarumi suke, yayinda shi kuma wanda zuciyar mugunta ne, sai ana masa kirarin Boss.
Har ila yau, akwai yan barkwanci, wanda kusan kowa yasan su da bada dariya, kwaɓa da yake a tattare da su, yakan sa masu kallo suji sunyi raha, koda kuwa a son ran su ba. Su waƴan nan, kamar gishiri suke a miya, wanda idan babu su to lamarin fim ɗin kamar ba zata haskaka yadda ake so ba.
Finaninai irin su, Inuwa, ɗan tawaye, Simgam, da kuma Bahubali, na daga cikin manyan Finaninai da suka shahara a Najeriya. Wnada kusan kuwa, koda ace Hausa fim kake kallo na ƴan Kannywood, zaka fahimci cewa 75 bisa ɗari suna koyi ne daga Indiya.
Ba iya nan ba, har yanzu dai, a bangare guda akwai soyayya, wanda kusan duk wani fim na Indiya, kamar doka ne, dole sai kaga soyayya, dabanci, nagarta, gwagwarmaya, darasi da sauran su. Soyayya ma na daga cikin abubuwa da sukayi tasiri a Nijeriya, wanda kusan zaka gani, soyayyar baya bayan nan, da kuka soyayyar kafin fitowar Indiya Hausa, akwai banbanci.
A wannan marhalan ne, matasa, da zamanin yazo lokacin da ake wannan fasaara, musamman wayan kafin fassara basu da wani wayo, sun taso ne cikin fassara ta Indiya, rayuwar su ya zamu gudunmawa daga fassarar Indiya Hausa. Wasu daga cikin su sun zama mutanen kirki. Domin sun koyi yadda ake karatu, da kuma yadda ake gwagwarmaya ta rayuwa. Wasu daga cikinsu, tabbas kallon da suke yi na finaninai ta Indiyan Hausa, yasa jin tamkar waliyai, domin sun samu natsuwa mai kyau, rayuwar su ta yelwanta, wanda kusan idan dai iyayen su, ba zasu iya basu wannan rayuwar ba kamar yadda Indiya Hausa ta basu.
Sai dai kuma a wani sashin na masu kallon, rayuwar su ya gurɓata, domin sun dauki salon ubbanin dada, wanda hakan yasa sun kasa fahimtar cewa a fim ne suka gani. Su ɗinnan, suna aikata abinda ya faru a fim a zahirance, ba tare da la'akarin cewa wannan fa ba gaskiya bane.
A kwanakin baya bayan nan, wani yaro karami da shekarun sa bai kai 10 ba, ya dauki wuka ya sa a wuta, bayan yayi ja sai ya ɗana wukar a bayan ɗan uwan sa, wanda yakan yayi ma ɗan uwan rauni.
Bayan nan, akwai wasu kalmomi da ake anfani dasu a fassarar, wanda shima yayi tasiri sossai a tsakanin matasa, musamman; zan sheƙe ka, zan gunduwa-gunduwa kai. Na suburbuɗe ka fa, zan halaƙa ka. Wannan fa a fim ne, to wasu matasa sun dauki abin kamar waƙa baki. Wanne yasa, a jihohi da ake fi kallon Indiya Hausa, an cika samun kashe kashe da matsa ke yi.
Misali a Maiduguri, kashe kashe na tsakanin matasan unguwanni, ya tsananta. Saboda kowa yana da daba da kuma uban daba, kamar yadda suke kallon abinda ke faruwa a fim ɗin Indiya.
Har ila yau, zaka ga matashi na da halaye irin na bosss ɗin Indiya, yana yawo da wuka, ya na magana irin na boss da babban murya, tare da shaye-shaye. Wannan, yana daga cikin manyan kalubale da ke addabar rayuwar matasa. Idan matashi yace maka zan kashe ka, to yaseen da gaske yake, dan kamar yadda ya gani a Indiya Hausa, an chakawa Yagi Babu wuka, ko adda, to haka zai chaka maka, domin baya tsoro. Ban sani ba, ko yana tunanin mutuwar nan ana zuwa a dawo ne? Ko kuma wukar na kisa ne ɗan wani lokaci a dawo. Sannan sai in bayan ya kashe wani bai dawo ba sai ya shiga cikin damuwa, tare da ma dama, shi kuma wanda ya mutu ya tafi, domin ba a fim bane, gaske ne.
Irin wannan, yana ta faruwa a Kano, kaga wani ya kashe uban sa, ko wani ya kashe mahaifiyar, ko ɗan uwan sa. Zaka na ganin daba, daba, daban-daban a cikin gari. Ba iya Kanon ba, gaba daya ilahiran garuruwa dake da tasirin kallon finafinai ta Indiyan Hausa, zaka fahimci cewa, soyayya na karuwa, dabanci ma na karuwa. Shekara da ta wuce, a Maiduguri, an samu kashe kashe irin wannan. A wata unguwa da ake kira Ngomari bayan Kostin, wani matashi mai shekara a 20 yazo wucewa, zai tsallaka kwakbeti, sai ya ɗan buga wayan wani matashi mai shekaru 16. Sai wanda aka buge masa waya yayi magana, shi kuma wanda ya buge y bashi hakuri. Da yake sun unguwa ɗaya, kuma sun san junar su, sai wanda aka buge masa waya ya cigaba da korafi, irin yaki hakura ɗinnan. Shi kuma wanda ya buge waya sai yace masa akan wayan ka burin kywaila dinnan ne kake min haka. Kamarin yayi tsami sossai, aka shiga tsakanin su aka raba su. Da yake shi mai shekaru 16 dinnan, yana aikin koyan ɗinki a shogon ɗan uwan sa, kuma shi ɗin maraya ne gaba da baya, ina nufin mahaifin sa da mahaifiyar sa duka sun rasu. Bayan an raba su, har fa ya koma shago, yana dinki, shi kuma dayan yana tsaye a tsallakin titi, kawai na cikin shagon ya fito da gudu ya chaka ma ɗan shekaru 20 sizos a wuya. Jini ya fara fitowa kafin a kai shi asibiti Allah ya karbi rayuwar sa.
Irin wannan kisa, ba sau daya ba, ba sau biyu ba abin na cigaba da faruwa, domin yanzu a Maiduguri, ko budurwa baka isa ka nema ba, ba tare da ƴan daba sun shata maka layi ba. Kuma su waƴan nan matasan, zaka ga yara ne, cikin su babu wanda ya shekarun sa sun haura 20. Sun gagari iyayen su, kamar yadda nace a farko, tasirin da Indiyan Hausa ke a zukatan su, ko iyayen su da suka haife su basu da wannan tasirin.
Batun soyayya, hakan yasa, uba yana kokarin koyawa yar sa tarbiya, tare da ganin ya killace ta, amman ina, kame kame, da aikin ɓatsa ba zai bari ba, domin sukan yi hakan ba tare da uban ma yasan anyi ba.
To zuwa yaushe za a kawo karshen wannan? Me Yakamata iyaye suyi game da tarbiyan ƴa'ƴan su? Shin hana su kallon Indiyan Hausa zaiyi? Wa yake da alhakin magance wannan lamarin? Bayan nan, idan har wannan bashi kaɗai bane matsalar da ke sa wa matasa suyi kisan kai, to menene ? Kai matashi Me ya kamata kayi ? Me ya kamata ma matashin yayi dan kauce ma wannan lamarin ? Mai karatu idan kana da bin cewa, zaka iya tuntubar mu dan ganin mun cece rayuwar kasar mu. Allah yasa mu dace.
