Bamu manta dakai ba Baba Mai Gwoza
Wanda baya kishin Gwoza ne ƙaɗai zai wuce baice Ameen ba.
Sarki abin alfahari, ya rayu cikin izza, kuma ya bar duniya da izza. Mai tausayi, da alkunya, ga tafiya na kasaita. Yau kusan shekara 10 kenan da suka kashe mana kai.
Rashin sa munji haushi da ba dadi, wanda da ana iya bada rai da mun dawo dakai. Mai daraja farin cikin masu daraja. Mai ilimi da shayarwa ga wayayyu. Ganin sa kadai yakan s
a nayi farin ciki, yanzu babu shi a duniya sun kashe shi.
Kasar gilla suka masa, da bulet suka masa, sun kona motar sa, ya tafi ya bar ƴaƴan sa, da kuma dangin sa.
Ina rubutu akan ka, tafiya yake kamar waka, hakan akai nake son kara zaka, dan nayi rubutu akan kisar ka.
Nayi a lokacin shekara shida, bani kadai ba wallahi harda, a newspaper aka madda, hakan yasa naji kayi shahada, Allah ya jikan masa sarkin Gwoza.
Zan iya kwana ina rubutu akan ka, nayi sati nayi wata har shekara, ban gaji ba kuma ban tsaya ba.
Allah ya bani baiwar rubutu, dashi nake alfahari, kuma daga garin ka na fara koya, wanda yanzu alhamdulillahi an sanni.
Kafin lokaci yayi, zan tattaki naje, wajen jinin ka nayi jaje, so nake naje har kabarin ka, na naka addu'a Allah jikan kaz Allah yasa kana cikin nima, su kuma makasan Allah ya musu abinda suka maka..
Baba uban marayu, yanzu ka tafi babu kai, babu dadi babu cigaba, na san da kana nan da mun fi haka cigaba.
Zamu cigaba Allah ya jikan Sarkin Gwoza.
#pressalbarno
Tags:
Gwoza Post
