Habu ya hau a tashar Alkhairi zai kuma sauka a tashar wulakanci
Habu ya hau a tashar Alkheri Direba na neman sauke shi a tashar Wulakancin
Labari mai tsawo, ya faru ne a shekara 50 baya, yayin wata tafiya mai tsawon Mil dubu biyar (50,000). Tafiya ce da darajar ta kai kwana 50, wanda ya kamata a isa idan aka dosa a kwana 25.
Habu yaro ne ƙarami, kuma wanda idon sa ya bude. Yana da zuciyar tausayi, gashi masanin hanya ne, wanda daman tun can yasa bin hanyoyi daban daban a nahiyar Afrika.
Tafiya ta kama yaro Habu saboda tashin hankali da ya faru a garin su, na dole sai yayi hijira da watarana zai dawo. Koda ya lallaba ya fito daga garin su, bai tashi samun mota ba saida yakai ga tashan Alkhairi.
Habu, ya samu mota mai kyau, babbace, dama bai taba ganin ta ba. Tana dauke da kujeru sama da 95, tana da kyau, ga da dadin shaani, wanda duk abinda yake so yayi dreban baida wani damuwa. Duk abinda yana so yayi na biyan bukata, kamar tsayawa pitsari, ko sayan abu, ko karbar sako, dreban baida damuwa zai tsaya dan ganin ya farantawa Habu rai. Hakan ya sake tabbatar ma Habu cewa lallai dreban nan mutumin kirki ne. Sai ya zage, ya sallama komai ga tafiyar dreban.
Koda tafiyar bata yi wani nisa ba, dolin ko Mil 50 ba akai ba, motar ta fara samun matsala. Babu pasinja, kuma ga hanyar akwai gargada, har saida ta kai ga motar ta samu matsala a hanya. Wasu ƙalilan oasinjoji da suke cikin motar sun fita, suna ta zagi dreban, yayin da shi Babu baiji dadin abin ba. Saboda ya za'ayi ace kamar Mr. Obi dreba ace baida mutunci? Wasu har zungura kai na Dreban sukayi, amman shi Habu ya tsaya kyen saboda ganin ya taimakawa dreba, tare da faranta masa.
Suka tsaya tare a jeji, yayin da kowa yaki ya tsaya ya taimaka musu, shi Habu yayi aiki tukuru wajen ganin motar nan tashi gaba da tafiya. Ba kai ga nisa ba, an shafe kwana biyar ba yawa, Habu ya haɗa da addu'a, tare datattara duk basiru da Allah ya bashi wajen taymakon Dreba. Bisa yardar Allah, ubangiji ya amsa addu'ar nan, mota ta tashi, kuma tafiya ta fara kyau. Sai Habu ya yanke shawarar taimakawa dreba dari bisa dari. Yace ma dreba, nasan hanyar nan, akwai ɓarayi, sannan ga gargada tayi yawa, kuma ba zamu samu pasinja ba, muyi dama, za a samu alkhairi, domin na taba biyowa wajen.
Dreba ya amince, domin lokacin duk abinda Habu ya faɗa masa zai yarda. Lokacin ko pasinja 5 babu a cikin motar, fargaba da tashin hankalin zaman daji ya sa sun rasa komai. Shine Habu ya tashi da kan shi ya zama kwandastan dole. Yayi da kiran pasinja, kan ace komai nan take sama da mutum 50 suka shiga mota. Ya tara kudi a wajen su, wanda ya bawa dreban, hakan yasa dreban farin ciki tare da son Habu. Sai dreban yaji a ran sa baya son habu ya sauka a motar, domin idan Habu ya sauka ba zaiji dadin tafiyar ba.
Daman Habu yana da inda zai sauka, kuma hijira ce tasa ya bar garin su, domin samar wa kai mafita. Yana da inda ya daso, amman saboda ganin yana son direban, kuma jinin su ta hadu, sai ya sallama masa da komai.
Oga Dreba ya samu kuɗi, aljihun sa ta cika makyel, wanda komai nasa na tafiya daidai. Ya samu ribar da bai taba samuwa ba tun da ya fara harkar tuki.
Da aka je wani gari, sai tsifofin abokan dreban su ma suka shigo tafiyar. Sun gaisa, sunji dadin ganin dreba cikin walwala. Sai suka ce masa me sirrin ne? Sai ya ce musu "in ana Sallah ba a magana). Sai suka ce masa gaskia ne Mr Obi ka samu lafiya. Sai suka tambaye shi wancan yaron fa? Sai yace pasinja na ne, wallahi yana da hankali ga kuma kirki, shine ya taymaka min lokacin babu kowa a tare dani. Yaron ɗan albarka ne, shine sanadin cigaban tafiya na.
Wasu abin yayi musu dadi, wasu kuma bai musu dadi ba. Dreban ya gaya musu komai yadda lamarin ya auku, da duk wahalar da suka sha. Sai suka ce masa, kai yaran yanzu ba abin yarda bane, domin mafi yawan su ɓarayi ne. Sai suka chanza masa tafiya, suka bashi shawara ya chanza hanya, kar yabi hanyar da habu ya bada shawarar abi. Yace a a, hanyar nan akwai Alkhairi fa, kuma za a ga Alkhairi. Hakan bai musu dadi ba, sai suka ce masa hanyar da muke bi, shekaran jiya, Ɓarayi sun kashe mutum 50, kuma ma ana tunanin zuwa gobe ɓarayin shanu zasu tare hanyar, kaga idan aka samu wata matsala, motar ka ta lalace kaga awaki damuwa. Motar fa bata lalace ba, kuma ba ama san mecece zata lalata motar ba, amman sun kawo wannan shawara. Da yake Habu, bako ne a wajen Dreba, ga abokai ƴan uba sun zo, sai ya fara biye musu.
Dreba ya chanza hanya, Habu ya same shi, yace masa, Oga Dreba, akwai fa damuwa a hanyar nan, ya kamata ka dauki mataki tin yanzu, sai yace masa a a, Allah ya ssauke mu lafiya kawai. Yace za a samu alkhairi a hanyar nan. Alkhairi bata samu ba, pasinja sun fara sauka, kuma wasu basu zo ba.
Abkona dreban, suka ce masa, wai ma ina ka samu Habu din nan ne? Sai suka ce masa ai Habu din nan barawo ne, ya kamata a karba kudin ka wajen sa. Sai Dreba ya karbo kuɗin sa duka, daga hannun Habu, ya basu amana. Sai suka fara zargin Habu, yana masa ganin kamar ma shi din Ɓarawo ne. Habu yana son ya koma gefe, amman abin ba zaiyu wu ba, domin idan ya koma gefe za a ce masa tabbas yayi sata din da gaske.
Tuni dai motar ta soma tangar tangar, babu pasinja, sai dai barayi ne ma ke shiga motar. Tabbas habu ya hango wani abu, idan ya yi kokarin gaya ma Dreba sai ga ba dadi, idan yayi shiru tafiyar ba zata ƙare lafiya ba. To yana son ya sauka ya hau wata motar, idan yayi hakan za ace nasa shi din barawo ne da gaske. Abin ya tsawa Habu a wuya, kashin kifi shi baije ciki ba kuma bai fita waje ba.
Tafiyar na ta tafiya, zargi na karuwa, rashin jin dadi sai karuwa. Dreban bai gamsu ba, kuma Habu ma bai gamsu ba. Yana son ya sauka, amman dreba yace masa ba anan yake son ya sauka ba, ya bari dai sunje tasha ta gaba.
Tasha ta gaba itace tasha ta Wulakanci, wurin da yan kashe wando ke hukunci, wajen ne jahilai ke sarauta, azzalumai ke tabbatar da doka. Wurin ne idan ka sauka, ko baka da komai sai an tursasa maka ka kawo. A wurin ne za ake sa mutum ana kuɗin dole. A wurin ne dole sai kayi kashin dola. Koda da a bakin duniya aka haife ka ba, dole sai kayi kashin naira. Koda ace ba zaka iya yi ba, to dole ne sakayi hakan.
Yanzu taymakon da Habu yayi wa dreba na neman tashi wa a tutar zero. Bai isa inda yake son yaje ba, kumq bai biya bukatun sa ba, bai sauka ya hau wata motar ba, gashi ana dole na neman ya sauka a tashar da tama fi garin ta taso ƙuna.
Ga shi kuma direban, hanya ta fara kure masa, baima san a yaya zai kai ga tashar Wulakanci din ba. Ya dai san zai tarar dasu shagurɓau, amman bai san a tayaya lamarin zata ƙaya ba. Habu yayi imanin cewa ko ina akwai Allah, baiji tsoron sauka a wurin ba, amman yama fi tausaya wa dreban, domin yasan masu bashi shawarar basu ba son cigaban shi suke ba, shi yana so ya sauka ya hau ga wani motar, wata ƙila abin zai so da sauki.
Zamu ci gaba Insha Allah.
Moral:
Mai karatu, ko ina idan zaka yi aiki da wani, kar ka yarda ku fara aiki da wani ba tare da kunyi shi da yarjejeniya ba. Ko kayi masa aikin a kyauta, ba tare da ka tsammace ya baka kuɗi na sallama ba, ko kuma kace masa ga abinda nake son ka riƙa biya na. Idan kun rattaba hannu to abin zai zo da sauki. Domin ɗan adam butulu ne, wasu shaidanu ne ke musu huɗuba, kar ka dauki kowa mai taymako ne irin ka. Zaka iya tausaya ma wsni5
dan Allah, amman zai tausaya maka saboda ribar da zai samo daga gare ka.
Tags:
Fiction
