Shin da gaske ne ina daukan kaine wani abu?
Shin da gaske ne ina daukan kaina wani abu?
Maganar gaskiya ba haka bane. Wani lokaci idan kaji wani abu ba girman ka bane ka maida martani akai. To amman wani lokacin yana da kyau kayi bayani akai, ko ba dan masu fada ba, don wasu da basu san ka ba kuma suna bukatan sun waye kai.
Kamar yadda nace, maida martani ba daidai bane, a lokuta da dama wasu da suke aikata magana akan mu, sai mu kyau nadan komai ba face babu lokacin sauraron wannan abu. Domin me, domin tsayawa da kuma ji da martani ga abin da wani ya faÉ—a akan ka ba daidai bane, dokin bata lokaci ne. A kullum idan wani yaga nayi magana mai kama da martani ga to ba martani face nunawa wasu halin da ake cikin don su rika sanin yadda zasu rika É—aukan mutane.
Wanda nashi da uba burin sa ya samu abinda uban sa ya kamata ya bashi idan yana raye, amman bashi da lokacin karya ko nuna kai ga abinda bashi da shi.
Wanda bashi da ilimi, kullum neman ilimi yake, jahili ne ke ganin cewa yanzu ya wadata da ilimi. To ina mai neman ilimi da kokarin hada kan shi da wasu ?
Talaka kullum neman yake, bai kamata wanda bashi da kudi yaje yana nuna kan sa shi wani ne. Daukan hoton karya, nuna kai, ko daukan gidan wasu a matsayin gidan ku hasara ce babba. Domin yaudara ce da ba zaka san da wannan ba sai ka girma, ina nufin da girma anan manyanta.
Mai hankali shine wanda kullum gina gaban sa yake da da al'umma, bai kamata ka riƙa anfani da lokaci da kake ciki yanzu ba, domin akwai lokaci da yake zuwa nan gaba, wanda tun yanzu ake ginawa, inma mutuwa ko rayuwa.
ÆŠaukan kai a matsayin masani, yafi hadarin akan É—aukan kai a matsayin wanda bai san komai ba alhalin ya sani.
Abota da jahili asara ne, haka kuma tursasa kai akan sai ka zama wane asara ne.
Ako da yaushe burina shine gina rayuwa ta, da yan uwa na, da abokai na, da Muminai, harda ma nakiya na. Bani da hasada ga samun wani. Saboda nayi imanin cewa Allah ne mai bada wa ga wanda yaso, to me zai sa naji haushi dan wani ya samu abinda ban samu ba ?
Kullum nakan kasance cikin bakin ciki da zarar naji wani abin bakin ciki ya sami wani. Burina shine adalci ga kowa, ban da mu ba koda wani ya zalunce baya daga cikin abin ambato na.
Ni kaina nasan ina nakiya, amman hakan ba zai sa nayi musu adalci ba. Daga cikin adalci ne akwai uzuri, sannan akwai daukan mataki, sannan matakin kauracewa da kuma matakin yanke hukunci.
Bana son damuwa, bana shiga harkar kowa. Walau ka so ni, ko ka kini, wasu zasu so ni. Shi hali shine abokin tafiya, din inda kaje zai kasance tare dakai. Ana iya rabuwa da kudi amman ba a rabuwa da ilimi.
Bana daukan kaina a matsayin wane, bana da ra'ayin dole sai na sa kayan da wane ke sakawa, ban iya roƙo ba ko zan mutu da yunwa. Kullum asiri na a rufe, wasu har gani suke na wadata ne, wanda da zasu ji halin da nake ciki babu wanda hawayen sa ba zai zuba ba. Godiyar Allah muke, kuma da shi na dogara.
Ni da nake maraya, me zai kaini yin rayuwa irin masu uba? A kullum tsoron shiga cikin mutane nake, domin bana so rayuwa irin nasu. Kullum ina neman wanda zai min fada, amman babu, sai dai a rika magana na a gefe. Bana maganar kowa a bayan idon sa, idan hakan ya faru to ina iya fada a gaban idon mishi.
Kullum burina hada zumunci nake, ban taba raba zumunci ba. Mutum nawa suka san junan su da wani saboda Ni? Mutum nawa sun zama abokai saboda Ni? Mutum nawa suka karu da junan su saboda ni? Chigaba shine farin ciki na. Bani da wani buri a duniya kamar naga kowa da kowa ana zaman lafiya.
Allah yayi min baiwa zama da mutane, wanda kusan zan iya cewa kusan mafi yawan yarukan Nijeriya ina da alaka da su. Mu dauki Hausawa, Igbo, Nupe, Igala, Karekare Fulani, Yoruba, kwarawa, Kanuri, Shuwa, Adamasa da Calaba. Harda baturai da larabawa duk mutane na ne. Kowa a duniya in ba azzalumi ba mutumina ne.
Ko wanne sati ina samun sanin abokai na zama, kuma ina ilmantuwa daga koramar su. To yaushe ne na dauki kaina wani?
Ina da Ƙa'ida, da tsare-tsare na rayuwa, ba ina rayuwa hakanan kawai ba. Wannan halin dashi nazo duniya, kuma dashi zan koma. Bai kamata mutum ya zauna baida tsari nashi na rayuwa ba. Shi yasa a ko yaushe idan aka kawo min maganan sani bana daukawa. Wani baya haɗa da wani martine inji barebari.
To, ba a iyawa mutane, bari nayi addu'a. Ya Allah idan har ina daukan kaine wani abu Allah ka yaye min, ba daukan kaina ya kamata nayi ba, aikin yakamata nayi. Ma'ana na nemi ilimi na dauki kaina kamar wanda bashi da ilimi, kuma nayi aikin ilimi. Idan kuma ba haka bane, Allah ka kara daukani, daukakar da zaka min nafi na wanda zan É—auki kaine, su kuma masu zargi Allah na yafe su, kaima ka yafe musu, hakan kuma ba zai taba sawa na daina son su ba.
Hawaye dole zai zuba, zuciya zata ji wani iri idan suka ji wani iri amman Allah da tsarkaka zukatan mu, kasa muyi wa kowa uzuri.
Tags:
Albarno
