​KISHI DA ILLOLINSA GA ƊAN ADAM



Daga Ali Adam Gobirawa (08139484263)


   Kishi wata ɗabi’a ce da mutum ke tsintar kansa a ciki, wanda shine zuciyarka ta ringa hararo maka abubuwan da wani ko wata suka mallaka, kaima kaji a ranka cewa kana son wannan abubuwan, ko kuma idan mutum ya zarce ka ta fuskacin wadata, farin jini a cikin mutane, shahara, ilimi, sanayya da sauran su, ka ringa jin cewa meyasa kai baka da abu kaza? Duk waɗannan ni’imomi ne da Allah yake bawa bayinsa wadanda ya so, sannan ya hana waɗanda ya so ba don waɗancan sun fi su ba. 


   Kishi kala-kala ne, akwai wanda yake da amfani, akwai kuma marar amfani kuma mai cutarwa wanda zai iya kai mutum ga fushin ubangiji, tareda halaka (wannan zamuyi magana akai). Shine wanda idan mutum ya biyewa son ransa wannan kishin zai juye zuwa ga hassada ba tare da mutum ya lura, ko kuma ya sani ba. Sannan mun san hassada itama wani ciwo ce ta ruhi, wanda yake sakawa mutum ya ringa tuhumar ubangiji akan ni’imomin da yake yiwa wasu bayinsa. A zahiri kishi akwai inda yake da amfani ga mutum, da rayuwarsa ma gabaɗaya, haka nan akwai inda yake baida amfani, zai cutar da rayuwar mutum ne.


  Sau dayawa zaka ga a cikin danginku, ko kuma abokan rayuwarka wasu sun yi maka nisa a fannin cigaban rayuwa, hakan ba yana nufin sun fika a wajen ubangiji bane, kamar yadda Manzon Allah (S) ya ce, “babu wani bawa da zai roqi Allah wata buƙata face an karbi addu’ar nan tasa. kodai idan ya tambaya za’a bashi a duniya, ko a yi masa tanadinsa ranar ƙiyama. wani lokacin kuma za’a yafe masa zunubansa ne a matsayin wannan abun da ya tambaya, ya danganta da irin abinda ya roƙa indai har bai zamo mai gaggawa ba.” Sai aka tambayi Manzon Allah cewa, “Ya Manzon Allah, taya bawa zai zama mai gaggawa?” ya amsa da cewa: “idan ya ce, “na roƙi Ubangiji, amma bai amsa min ba’”. A nan zamu gane cewa kowa akwai irin tanadin da Ubangiji ya yi masa, kodai a nan duniya ko kuma a lahira. Saboda haka duk abinda kaga wani ya samu ka kauda idonka daga hangensa, domin Ubangijin da ya bashi kaima bai manta da kai ba.


                 RASHIN WADATAR ZUCIYA


  Daga cikin illolin da kishi ke haifarwa akwai rashin godiya ga Allah, da kuma wadatar zuci. Idan mutum yana da irin dabi’ar nan dayawan lokuta zai ringa mantawa da irin ni’imomin da Ubangiji ya yi masa, sai ya ringa hangen na wasu, har ma ya ringa jin cewa dama shine yake da kaza, ko kuma dama shine a matsayin da wani yake. Hakan kuma zai janyowa mutum fushin Ubangiji ne, domin Allah ya na son bawansa mai yawan godiya akan ni’imomin da yayi masa. Kamar yadda yazo a cikin Qur’ani mai girma; “wa’iz ta’azzana rabbakum la’in shakartum la azizan nakum, wa la’in kafartum inna azabi lashadid” wato ku tuna cewa, duk sanda Ubangijinku ya baku, idan kuka gode masa zai ƙaro muku (ni’ima), idan kuma kuka ƙi, tabbas azabar Allah mai raɗaɗi ce (suratu Ibrahim, aya ta 7). Akwai kuma inda Allah yake cewa: “wa ataakum min kulli ma sa’altumuhu. Wa in ta’uddu wa ni’imatallahi la tuhsuhaa. Innal insana la zalumun kaffar”  ...Sannan yana baku daga dukkan abinda kuka tambaya. Da zaku ƙirga yawan ni’imominsa gareku ba zaku iya sanin yawansu ba. Lallai Dan Adam butulu ne kuma marar godiya (suratu Ibrahim, aya ta 34). A nan zamu fahimci cewa kishi akan abinda mutum bai mallaka ba, ɗabi’a ce ta Dan Adam. Kuma Ubangiji baya son masu irin wannan halin.


  Duk lokacin da ka lura zuciyarka tana kawo maka irin wadancan abubuwa, ka gaggauta dakatar da ita, tare da neman tsari daga shaidan domin shi mai ɓatar da mutane ne. Ka tuna cewa Allah shine Ar-Razzaqu (wato mai azurtawa), Al-Fattahu (mai buɗewa ko mai bayarwa), sannan kuma shine Al-Karim (mai karamci). Taskar ubangiji koyaushe a buɗe take ga bayinsa, sannan bata taba ƙarewa, indai har zaka tashi ka nema kuma ka roƙe shi zaka samu rabonka, saidai ba lallai ne ya zo ta hanyar da kake tsammani ba, wani lokacin zaka roƙi Allah wani abu ya chanza maka da mafi alkhairy. Saboda ya fika sanin abinda zai zamar maka alkairy a rayuwarka. Kar saboda wani ya samu irin abunda kake so kaji cewa kai ba zaka samu ba, taskar Ubangiji tana dayawa kuma bata taɓa ƙarewa, kaima zai iya baka fiye da wannan abun.


  Kar ka zama mai tuhumar Ubangiji saboda bai baka dukiya dayawa ba, rashin dukiya dayawa ba zai hanaka farin ciki da kwanciyar hankali ba, amma yawaita damuwa akan hakan zai janyo maka damuwa sannan ya hanaka ganin abinda kake dashi. Haka rayuwa take, dole ne wani zai fi wani. Koda a wajen aiki ne kar kaga wasu suna ta samun cigaba hakan ya dameka, kaima idan ka dage tare da yin addu’a Ubangiji zai ɗagaka sama. Ka faɗawa zuciyarka cewa, “Allah yana sane dakai, bai manta dakai ba.”

  Domin gujewa rashin wadatar zuci, ka tsaya, ka nutsu tare da fahimtar irin baiwar da Allah ya yi maka a rayuwa, kamar yadda kowa yana da irin tashi baiwar. Ka kauda tunanin abinda ranka yake so alhalin ba zaka iya samun sa ba, ka maida hankali akan wanda kake dashi. Hakan zai sanya maka nutsuwa sannan zaka san abinda zaka iya da wanda ba zaka iya ba. Ba lallai ne baiwar ku tazo ɗaya da abokanka ba ko wanda kake kishi akansa, Wasu Allah ya yi musu baiwar iya rubutu, idan irin baiwar da kake da ita kenan sai ka yi amfani da ita domin samun daidaito a rayuwarka. Wasu sana’ar hannu Allah ya basu baiwarta, idan kana ciki kaima kayi amfani da ita domin chanza rayuwarka. Sannan ka saka a ranka cewa, don kawai wasu basu muhimmantar da irin baiwar da Allah ya baka ba hakan ya saka kaji batada amfani.


  Idan kana son samun wadatar zuci, ka chanza irin tunanin da kake yi a cikin ranka, daga tunani marar kyau (negative thinking) zuwa mai kyau (positive thinking). Ka maida hankali akan yanda kake magana da kanka. Idan ka zamo mai tunani marar kyau yanayinka zai nuna hakan, kamar yadda idan tunaninka mai kyau ne shima zai nuna hakan a yanayinka. Misali, kana zaune sai wani ya zo yana ta fadin abubuwa marasa daɗi a kanka, yana faɗa maka maganganu marasa kyau, ya zaka ji a cikin ranka? Dole ba zaka ji daɗi ba. zaka ji haushin sa kuma zaka shiga damuwa. Idan wannan mutumin kaine kake faɗawa kanka haka fa? lallai chanza irin tunanin da kake yi a cikin ranka daga marar kyau (negative self-talk) zuwa mai kyau (positive self-talk) yana taka muhimmiyar rawa wajen chanza salon rayuwar mutum, tare da sanya nutsuwa a tare da mutum.  

            

  ƘISSAR HABILA DA ƘABILA


  Baƙin kishi ko hassada, sun samo asali ne tun farkon bayyanar Dan Adam. Kamar yadda ya zo a tarihin musulunci da kuma wasu daga cikin kiristoci, mun ji labarin yanda ‘ya’yan Annabi Adam Habila da Ƙabila suka gudanar da sadaukarwa, amma ta da


ɗaya ce kawai ta karɓu. Ta dalilin hassada, Ƙabila ya kashe dan uwansa Habila wanda hakan ya sanya shi nadama. Ƙabila ya fuskanci wasu abubuwa guda uku, bayan kashe ɗan uwansa, wanda sune: 


- Ya yi dana sani akan irin baƙin kishin sa, wanda ya janyo kashe ɗan uwansa,


- Sannan ya zamo mutum na farko da ya fara aikata kisan kai,


- Sannan ya ɗaga matsayin ɗan uwansa, inda ya zamo Shahidin farko a musulunci.


  Hassada da kuma kishi, suna daga cikin abubuwa masu ƙarfi da suke janyo ciwon ruhi da kuma mummunar barna ga alaƙa. Munji dai gajeruwar ƙissar Ƙabila da Habila, waɗanda ‘ya’yan Annabin Allah ne, amma kishi da kuma hassada suka taru waje daya suka sanya Ƙabila tafka babban kuskure, ya zamo jinin ɗan uwansa ya rataya a wuyansa. Indai dan Annabi zai iya aikata kisan kai dalilin hassada da kuma kishi, to ina gamu? Waɗannan dabi’oine masu cutar da lafiyar ruhi, zuciya, rayuwar mutum da kuma wasu mutanen ma gabaɗaya. Mu yi ƙoƙari wajen ganin mun rage irin yanda muke daukar abubuwa a cikin zuƙatanmu, domin hakan zai bamu damar gudana da rayuwarmu cikin aminci, da kuma kwanciyar hankali.