Matsayin munafuki a waje na
Daga Mohammed Albarno
Munafuki shine wanda aka san shi da kirkirar hade-hade. Shine wanda a ko yaushe yana jiran wani ya fadiagana ko ya aikata wani abu dan yasamu abin bada labari ga abokin adawar mutum.
Yana daga cikin dabi'ar munafuki, kai magana da kawo wa. Zai baka labari, shiki harda gaskia da karya, haka zalika zai dauki naka, ya kai ma wanda akayi maganar sa. Kaga ya tursasa ka, kace wani abu, sannan kuma ya tattare duk wani abinda ka fada ya Kai wajen da ma baka da tsammani.
A irin wannan halin, munafuki yana hada rigima tsakanin mutane masu zaman lafiya. Ko batawa mai mutunci suna a idon duniya. Ko kuma, yana daga cikin aikin sa, gulma da rada, da wasu aikace aikace na da Allah ya hana su. Duk wayan nan aikin munafi na daga cikin abubuwan da Allah yayi Hani akan su. Misali Allah ya yi gargadi kan munafunci, waton kai magana da kawowa.
A karo guda, ni munafuki yana burge ni. Domin yana daga cikin media da ake anfani dasu wajen isar da sako. Kamar yadda kake ganin radiyo na isar da sako ta hanyar murya da lonaci, yayin da kuma jaridu na daga cikin muhalli na isar da sako ta hanyar bugawa da shafi. Haka shima munafuki na daga cikin masu isar da sako ta hanyar tattaki ko murya. Shi yasa ma masu iya magana suna masa kirari da radio mai jini.
Wani hanyar isar da sako da munafuki ke anfani dashi shine. Watakila kai kana bayyana abin da ya dame ka ga wasu, yayin da shi kuma munafuki zai dauki maganar da muhimmanci dan ya isar ga wanda ya maka laifi.
Munafuki yana da wani dabi'a, zai gaya maka labarai masu dadi, masu ratasa zuciya, wayanan labaran duk basu faru ba. Kai zai iya ma faruwa, amman shi kawai jira yake kace uffan sannan ya kai ga wanda yake maka magana akan shi.
Munafuki, wani mutum ne da baya son zaman lafiya tsakanin mutane. Wadannan mutanen, zai iya zama ma'aurata, ko abokai, kai yan uwa, tsakanin abokai, kai har ma tsakanin Da da iyayen sa.
Saboda haka, mu kula zama da munafu7, musan su wanene munafukan mu, su wanene masoyan mu. Mu san irin maganar da zamuyi a wajen munafikan mu, da kuma masoyan mu. In ka koyi zama da munafuki to ka kama sanin halin rayuwa.
Bai kamata na sauka ba, ba tare da nayi nasiha ga masu aiki irin na munafurci ba. Munafurci bata da riba, kar ku biye wayanda Allah ya tsine musu. Duk wani munafuki Allah ya tsine masa, kar mu zama masu tsinuwa sabida munafurci. Mu zama masu kwantar da tarzoma ba masu rura wutar ta ba.
Allah ka tsare mu da Sharrin munafuki, ka kuma kare mu da aikata munafurci.
Ameen