Yawan Accident: ya kamata a hana Napep hawan Express

Yawan Accident: ya kamata a hana Napep hawan Express 

Daga Muhammad Albarno 

Maiduguri ya fara cika za a ce an fara samun cigaba, kuma ga duk garin da aka samu cigaba Keke Napep ba sa hawan Express, dalili hakan gujewa mummunan hatsarurruka. Kamar Abuja, Lagos, da sauran wasu yankuna da suka hada da wasu baadin jihohin arewa.
Wannan shine karo na biyu da aukuwar hatsari mafi muni a birnin Maiduguri; na farko, hatsari da ya faru a Kwastom, daidai junction na Ngomburu, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama. Kuka wa'yanda suka rasu din zaka ga akwai keke Napep a ciki. Sai wanda ya auku na baya bayan nan, a Bolorin Round About, wannan kam yafi muni ma, shima zaka ga wa'yanda abin yafi shafa yan kake Napep ne. Inda aka bari iya nan, to lamarin zai ci gaba da aukuwa, wanda kuma anyi ta rasa rayuka kenan.

Babbar mota, tifa, treloli, da sauran su, mafi yawan su ana samun matsalar breki gare su, koga yaki kamawa, ko ya tsinke, da zarar daya daga cikin biyu dinnan ya samu shikenan sai hawa kan duk wani abin da yake gaban shi.

Keke Napep da manyan motoci, sam sam bai kamata su hada hanya ba, domin da zarar breki ya tsinke ma babbar mota, to ganin keke Napep yake kamar tauka. Kar ku manta, keke na daukan mutane 3 a baya, uku a gaba da direba, jimillah 6 kenan. Babban mota idan yazo a guje na iya markade keke Napep 3 kafin ya tsaya, kayi tunani ka gani, idan hakan ya sake faruwa, mutum nawa zasu mutu idan aka taka keke 5 a lokaci guda?

Har ila yau, ba yana nufin a hana keke gaba daya a Maiduguri ba, a a, a kayyade, kamar wasu manyan titunan da manyan mota sun cika hawa, sannan keke suna bi, ya kamata a hana aukuwar hakan. Sannan yankunan da ba express ba, keke na iya bi, na iya aiki a wurin, hakan shima cigaba ne.

Rashin keke da abinda zai haifar, na'am, keke Napep na da kyau, domin matasa da yawa na amfanuwa da shi, wajen samun kuɗi, kuma rufin asiri. Wasu zasu yi tunani idan aka hana kamar matasa da yawa zasu rasa aikin yi. Ba haka bane, bari muyi shi dalla dalla.

Idan aka hana keke, ba ana nufin an hana aiki gaba daya bane, a a, za a iya chanza salon aikin, misali, a sanya manyan titunan da keke ba zasu hau ba kamar haka; Airport zuwa Post Office, sannan zuwa West End, daga West End zuwa Custom, zuwa University Bama Road. Sannan titin Lagos Street, zuwa gidan Madara zuwa police Round about. Hala zalika zuwa daga Polo zuwa Post Office. Iya wa'yannan ya kamata a hana keke bi.

Dame za a musanya keke Napep? Akwai Buses, kamar kirar hayis, basu ma kai keke Napep a kudi ba, suna da girman da, ko babban mota zai ji tsoron ya take su, ba kamar irin keke ba. Kamar kurokwe, wanda aka fi sani da kiriku, ko kuma irin motocin Zulum dinnan, hakan zai taima wajen ciyar da gari gaba, da kuma samun nasarar dakile sace sacen wayoyi da ake yi a keke, da kuma hatsari da ake yi.
Ina ya kamata keke Napep suyi aiki? Wannan zasu hada ne da irin su, London zuwa bakin hanya, Kaleri, Yankunan kasuwa, hausari, da sauran titunan da ba express ba. Amman express a barwa motocin da ba Keke Napep ba.

Kuyi hakuri fa, ko wane chanji baya zuwa da sauki, wasu zasu yi tunani kamar bana son cigaban keke Napep ne, a a, ko kadan, chanji ake nema, domin hakan zai taimakawa al'umma, sannan harkokin kasuwanci zasu bunkasa. Hatsarurruka zasu ragu, gari zai samu cigaba. Za a musanya keke da motocin buss.

A karshe, ina mika sakon taaziyya ga iyalan wa'yanda suka rasa rayukansu, Allah ya baku hakurin kasance wa ba tare da su ba, ya kuma gafarta musu, ya musu rahama. Fatan idan namu yazo mu cika da imani.