Gwoza: Bai kamata rashin tsaro ya hana aiki ba

Wannan garin Shinkafi kenan, garin da Bello Turji ya taso, garin da yan bindiga sun hana kowa sukuni, garin da kowa yake tsoron rayuwa a ciki, garin da Turji yake yanka mutane kamar rago. Duk da haka bai hana anyi musu ayyukan cigaba ba. 
Mu a Gwoza an fake da rashin tsaro, an bar mu a baya, har yanzu babu gaba, babu babu baya. In kayi magana sai ace ai babu zaman lafiya. Shekara 20 yau da sani na hanya, har yanzu firgi yana nan a firgicin sa. Cikin gari ana ta rudin mu da fake project. Nawa senator yake karba a wata? 21.m+, in kayi sau 12 lissafin ba karami ba. Wannan kadai ya isa a samu cigaba a garin mu yankin mu. Da zarar kayi magana, wasu da basu san kudi ba, an rufe musu ido da 30k sai suce sai wane? Nawa rep yana karba? Dan majalisar jiha bai iya kawo cigaba ko kadan ba, amman wasu saboda son kai sai suce yayi mana kokari. 

Suna cewa, Gwoza kam Alhamdulihh an samu cigaba? Dole ai, shi wanda ya fito daga dutse zai ce an samu cigaba, Amman wnada yasan menene ma'anar cigaba ba zai taba kiran wannan cigaba ba. 

Kullum in mun je wajen Gwamna, babu mai magana akan garin sa da al'ummar sa, kowa cikin sa yake dubawa. Wasu a ra'ayin su, da a kawo cigaba Gwoza gwara cikin su ya samu gaba, akan al'ummar su. Shi yasa mukayi ta dawwama a yanayi da muke ciki. Gwamna zai dan wani war-war nasa, zai kaji al'umma suna ta murna. 

Wai ni kam baku san ce wa hakkin ku bane? Kuna jin dadi zuwa Lagos da Abuja da yayan ku suke yi ne? Kuna jin dadi yadda muke zuwa mu sayar da kwaya dinnan ne? Mutum nawa shuwagabannin nan suka kawo musu cigaba? 

Maganar gaskiya, ko kuna so, ko baku so, wayan nan ba zasu yaba chanja muku rayuwa ba. Saboda basu kawo makarantu na zamani a Gwoza ba, ka taba garin ya'yan su suna makaranta a Gwoza? Ka taba ganin matan su suna zama a Gwoza? Sai Abuja da garin wani, an bar masu kwadayi da zuwa nara a gidan manya. 

Wani lokaci abin haushi ma, kudin da za a baka, ko kudin motar da ka kashe ba zai biya ka ba. To ina suke kai kudin nan? Suna karba, suna ci, kuma zero project, daga su sai ya'yan su, da yan bangan su. Shi yasa garin su ko oho. 

Da zarar kayi magana sai a baka barazanar kisa, ko ace za a boye ka, su kuma matsorata sai suce a a, gwara mu karba, mu tsira da ran mu. Ko wane rai zai dandana mutuwa, da taruwa shekara dari kamar rago karkashin zalunci, gwara rayuwa kwana 1 kamar zaki cikin izza.

In zaku gyara ku gyara, in ba zaku gyara ba, nan gama zamu baje salarin kowa a paranti. Tsage gaskia na farko har zuwa ila masha Allah zai biyo baya.

Allah yasa mu dace, ya daukaka Gwoza. Allah yasa shuwagabannin mu su gane, su mana aiki na kwarai. Allah yasa su kori makwadaita, Sannan su mana aiki na kwarai.