Ana wahalar shiga mota a Borno
A che-chi al'ummar Borno kafin labarin mutuwa ta riske ku.
Daga Mohammed Albarno
Gari yayi zafi, ta ko ina ya ɗauki ɗumi. Rayuwa na sake yin tsada, komai nata karanci, hakan yasa dole sai an shiga motar Zulum, wanda chunkoso yayi yawa, hakan na iya sa mutane su rasa rayukan su.
Kwamishina mai kama da agogo Sarkin aiki, wanda yana tare da Gwamna mai alfarma kuma mai tausayin al'umma. Nace tausayi, wanda kowa ya sani kuma an gani, kuma lallai an shaida. Ba a kammala wanka sai da sabulu, dole a duba lamarin nan, dan gyara adon amarya a gaban angon ta.
Abubuwa da ke faruwa;
1. Mutane na tururuwa cikin motar nan, ana matsi sossai, kujerar da ya kamata a dau mutum biyu ana daukan 3. Babu iska mai kyau, ga mata, ga masu goyo, wallahi harda mace mai ciki na bin sahun shiga motar nan.
2. Cin mutunci drebobi ga marasa galihu. Na taba shiga motar, naga wani dreba yana zagin mata tsofi, kamar yara kanana, wallahi ciki harda wanda ta haife shi, na zubar da hawaye ranar, abun ba dadi.
3. Na taba ganin wata mata, tazo da goyo, ga kaya aka, ga kuma zafin rana, tazo zata shiga motar, masu lodi suka tunkuɗa ta zuwa waje da kayan ta, na tambaya, cemin akai wai dreba ne. Yana ta rantsuwa ba zai dauke ta ta, wallahi naji takaici sossai.
4. Su kan su drebobin, suna cikin yanayi, fasinja zai iya sauka anan, wani kuma a gaba kadan. Kuna wasu na kokawa game da tsarin na aikin na rashin mai, ko haraji da aka daura musu. Da wannan ne ma suke kafa hujjar yin lodi da yafi ƙarfin motar.
5. Barayi sunyi yawa, yanzu yanzu su shiga mota, badan komai ba face dan kawai su saci kayan pasinja.
6. Wani kalar kuɗi da ake anfani da su, na kasa gane wai inane wannan kudin ya fito. Musamman wajen neman chanji ana ta samun gagarumar masatala.
7. Rannan a motar nan, a wata sabon tsari da aka kawo, wai dole sai an zauna, gudun kar ayi musu maganar sun yi lodi mai yawa, direba yace kowa ya zauna. Ciki harda wani baban tsoho mai shekara sama da 50 zuwa 60. Dan Allah tayaya tsoho zai tsuguna? Tayaya mata mai ciki zata tsuguna a motar?
8. Watarana kuma, tururuwa da ake yi zuwa shiga motar, wannan rashin tsari ne, hakan yasa mutane da yawa na haduwa, kamar mata da maza, da dai sauran su.
9. Direbobi suna korafi, kamar kudin ya kasa, shi yasa suke daukan overload.
Hanyoyi da ta kamata abi wajen magance wannan!
A tunani na ya kamata ace;
1. A dawo da anfani da Bus-Stop, mutum ba zai sauka ba sai a Bus-Stop, kuma ba zai hau ba sai a can.
2. A kawo tsarin Lagos, jaha ai jaha ce, babu batun cewa namu ba a samu cigaba da za'ayi hakan ba. Mutum ya biya kudi a Bos-Stop kafin ya shiga mota. Zaka iya yin booking ma, hakan zai bada dama ga masu transfer, saboda yanayi da ake ciki ma rashin isassun takardun kuɗaɗe a hannu. Mutum ya biya kuɗin, yazo ya nuna takardar shaida, sannan a bar shi ya shiga mota. Hakan zai taimakawa pasinja da kuma drebobin motar.
3. A kayyade yawan mutane da motar zata ɗiba. Misali idan mutum 30 ne, to masu lodi zasu dibi iya mutum 30 sannan su tafi, wani motar kuma itazo ta ɗibe su. Hakan zai sa, a magance yamutsuwa da ake yi a cikin motar. Mai ciki zata samu sa'ada, raunana kuma a basu haqqin su. Tsofofin su srara mai kyau.
4. Drebobin su kula da haqqin mutane, banda cin mutunci, banda raina iyaye, musamman ma mata da suka haife su. Ga pasinja, bai kamata yazo yana cha-char baki da dreba ba.
5. Idan babu, ko ana karancin takardun kudade, tsarin yin transfer zai matukar taimakawa al'umma.
6. Domin magance wannan matsalar, gwara a kara kudin motar, daga #50 zuwa ₦100. Shima ba laifi, gwamnatin zata dan samu sauki, suma al umma a rage yaɗuwar cututtuka.
7. Bance ba, amma ya kamata, ban kuma ce dole ba, ko baayi tsarin ba yana da kyau. Wannan tsarin shine, tsarin dawo anfani da Kati, mutum yana zuwa kawai na'ura zata tantance shi sannan ya kwaɗe mota abun shi. Idan yazo sauka motar ta ce masa Goodbye legend, ko a sauka lafiya da Hausa, yayin da daman lokacin zai shiga ance masa welcome.
Wannan shine takaice mai girma kwamishina. Akwai tsare tsare masu yawa, wanda Yakamata a dauki mataki akai, kafin aji cewa zafi yasa wata mata ta mutu a motar Zulum. Ko ace wata ta haihu saboda cunkoso, ko ace jaririn yaro ya mutu saboda tirmatsitsi.
Allah yasa mudace, Allah ya kara lafiya, shawara ce ba umarni ba.
Tags:
Column
