Ziyarar Alincy zuwa ga abokin sa Albarno

Ziyarar da ba zan taba mantawa ba.


Shekara 4 da suka ce, watarana a wayanda November ta shekara ta 2017, na kasance a garin Maiduguri domin duba iyaye na. Bayan da na tashi komawa na tsaya a Potiskum dan na gaisa da abokai na, ciki harda Alincy, amman a lokacin baya nan a gari yana makaranta.


Bayan komawa ta gida Zaria, da wasu kwanaki ba mai yawa ba, wanda ya kasance a rana mai kama ta yau, 29 da kuma 30 zuwa 31 na watan December karshen sheka ta 2017, kawai sai ga kira daga Alincy, ya ce zai kawo min ziyara ta musamman zuwa Zaria, sannan zai hada da halarta auren Auwalu Lala.


Alincy abokina tin da dadewa, kuma a lokacin bamu taba haduwa ba, abotar mu yakai kololuwar da ba wanda zai iya yin kwana 3 ba tare da ya Kira wanin mu ba, amman kuma bamu taba haduwa ba, kawai sai gashi kwatsam a lokacin yace zai zo.


Tuni dai na fara wasu tunani da kowa ya zaba yi idan zasu hadu da wani, ina ta ce wa tayaya zamu hadu dashi, watakila yace ban dace a abokan sa ba, maybe yace hali na bai masa ba, gaba daya hankali ya tashi, kuma gashi tabbas ina son mu hadu dashi, saboda yana daga cikin mutum 3 na manyan abokai na da bani da kamar su a lokacin.


Da karfe 2 na yamma ya baro Patiskum zuwa Kano, koda yake bai iso ba sai da yakai karfe 6 na yamma, ga kuma ana lokacin sanyi, wanda duk wanda yake arewacin kasar mu Nigeria yasan irin tsananin sanyi da akeyi a wannan lokacin. Bayan maganar sanyi, akwai kuma maganar wahalar motar hawa da yake addan mutane a kasar nan. Musamman mota daga Kano zuwa Zaria, Kaduna, Abuja, wannan hanya na daya daga cikin wuraren da ake wahalar motar haya a wannan lokacin.


Bayan ya iso Kano, ga sanyi ga wahalar mota, bai samu mota ba, ga kuma sanyi, gaba daya hankali na ya tashi. Da yake ya tsaya a Na'ibawa Flyover, karkashin gadar zama da Malam Ibrahim Shekarau, wurin babu mota, haka zalika ya kara gaba zuwa kwanar dawaki ko zai samu mota. Nan ma kusan 11 na dare babu mota, har zuwa 12. Gaba daya hankalina ya tashi. Na nema yaje ko gidan wani Dan uwa da muka sanshi a Dawaki ya kwana sannan gobe ya sai shigo Zaria. To amman yace a a, domin wannan ziyar bai tsaro ta da sunan zai tsaya a wurin wani ba, wannan ziyar ta musamman ce dan ni sannan mu hadu.


Can anjima ba da jimawa ba, sai yace min yawwa ya samu motar zuwa Zaria, amman yace naje nayi bacci abina kada hankali na ya tashi, domin da asubah sai iso waje na. Gaba daya naje ina ta tunanin, wane irin hali yake ciki, sannan a yaya ma zan fara hada ido dashi, duk da nasan shi mutumin kirki ne, amman ina tsoron irin ziyarar da ke raba zumuncin.


Da wayewar gari ranar 30 ga wata, bayan sallan asubah, sai gashi ya kiran yace yana Danmagaji. Daman ya kashe wayar sa, domin idan ya bar wayar sa a kunne to zan kwana ina jiran shi, domin duk bayan mintuna 15 sai na kira shi na tambaye ko suna ina. Bayan na daga kiran shi, sai muka fito bakin titi wajen kofar kibo domin na tarbe abokina da na dade ina marmarin mu hadu dashi.


Bayan na fito bakin titi, a kusa dani akwai wani kanina da shima yana tayani a duk wani hali da nake ciki game da wannan ziyar, shima ya biyo ni. A lokacin, duk wani mashin da fito sai na duba naga ko Alincy ne a kai, sai naji zuciya ya tayi rass, sannan kuma ashe bashi bane. Can anjima mintuna kadan sai gashi yazo, da hula jaa akan sa, yana tsayawa kawai sai ya rungume ni, naje masa kai amman abokina kasha hanya kuma kasha sanyi.


Zan ci gaba insha Allahu zuwa gobe fatan zaku kasance tare dani kuji yadda haduwar mu na farko ta kasance tare da abokina Aliyu Zakar Ya'u, Alincy.