Yajin aikin ASUU na iya jefa dalibai aikin ta'addanci

Daga Jaridar Manhaja


Daga Mohammed Albarno


Miliyoyin dalibai ne suke zaune a gida ba tare da yin wani aiki ba, sakamakon yajin aiki da kungiyar malaman jami'a suka shiga tin 14 ga watan Febrarun 2022. A wata yunkurin da kungiyar tayi ikirarin ce wa suna neman hakkin su a wajen Gwamnatin Tarayya, wanda akalla kudin sun kai 8.b zuwa 1.t. 


Tin daga ranar 14 ga watan 2, dalibai na gida ba tare da suna wani aiki ba, hakan na iya zama baranza ga makomar su, domin komai na iya faruwa. Musamman nan kasar mu Nijeriyya, akwai wani dabi'a da ya zama wa kowa jiki, shine mutum ba zai iya zama haka ba, ba tare da yana aikata wani abu ba, koda kuwa aikin na Alkhairi ne, ko sharri. Wanda hakan nema yasa zaman gida a zamanin korona da kuma yajin aikin na ASUU ya haifar da annobar zangazanga. Anyi asarar triliyoyin kudade a kasar.


Idan mukayi duba tare kuma da nazari, game da lokacin da ASUU tayi yajin aiki na baya bayan nan kafin wannan, duk da cewa yajin aikin ya hadu ne da zamanin cutar Korona Vairus, wannan na daga cikin dalilan da suka haifar da rikicin #EndSars. Anyi asarar rayuka, dukiyoyi, dama kanta barazanar zaman lafiya ga ita Gwamnatin Tarayya.


Musamman dalibin jami'a, da ya zama cikin yanayi na zirga-zirga, zuwa ofishin kodineta, ofishin H.O.D, da sauran dakunan karatu. Yau idan aka ce babu abinda zai dauke masa hankali, maana Kwakwalwar sa baida damuwar komai, to zai kaga ya fara tunanin rubuce rubuce a social media wanda hakan na iya haifar da rigima a kasa.


Tasirin zangazangar #EndSars, duk da abin ya hadu da korona, amman babban abinda ya sa zangazangar gishiri yayi mata yawa shine, irin rura wuta da wasu korarrun jami'an Gwamnati suka yi wa dalibai, su kuma lokacin suna zama ne a gida babu aikin yi, kaga ba abinda zai hana su goya musu baya. Wanda da ace suna makaranta, mutum na fama da wahalar makaranta, ko yanayi na test ko jarabawa ko aikin gida, ba zai taba goyon bayan #Endsars ba, domin yadda za'ayi ya bar cikin jami'a ya goyi bayan zangazangar.


Hama a wannan karo, yanzu yajin aikin na gab da kammala mataki na biyu, na farkon shine matakin yajin aiki na gargadi ga Gwamnati Tarayya, wanda aka yi shi daga 14 ga wanda Fabreru zuwa 14 ga watan Maris, daga nan aka wuce mataki na 2 wanda ake tunanin lokacin sati 6 za ayi zama da tsakanin kungiyar ta Malamai da kuma Gwamnatin Tarayya. Bisa ga dukkan alamu dai, wasu bayanai na nuna cewa kamar za a iya zuwa yajin aiki na sai mama ta gani.


Yajin aiki na sai mama ta gani, ana nufin yajin aiki ne da ba a san ranar dawowan su ba, domin akan iya yin watanni sama da 5 ba tare da an dawo ba. Irin shi ne ya faru a shekara ta 2020, ma'ana yajin aiki na zamanin korona, wanda shine ya haifar da zangazangar #EndSars.


Idan aka ce dalibai zasu ci gaba da zaman gida, komai na iya faruwa. Duk da cewa su wayan nan korarrun jami'an Gwamnati din, gaba daya wukar su ya koma kan siyasar da ake fuskanta, amman hakan ba yana nufin wani shaidan ba zai zo ya kunno wata wutar rigima ba.


Tuni dai wasu mutane da sun fara runa mi'arar da zata iya biyo bayan kaulasar a wannan tafiyar ta yajin aiki. Shugaban HEKAN Kiri ya ce "yajin aiki na iya tura dalibai fadawa cikin aikin ta'addanci". Dama sauran mutane makamancin sa.


Mafita, ana kashe gobara ne kafin wutar tafi karfin ruwan da ake nema na kashewa. Sannan, yakamata Gwamnati ta kawo karshen zaman dalibai a gida, ta tausayawa iyaye, ta kuma cece kasa daga fadawa cikin rikicin da zai haifar da asarorin kudade. Idan aka ce Gwamanati bata da kudin da zata kawo karshen bukatar kungiyar malamai ASUU, tayi tunani mana, abinda zai iya biyowa baya. Akan yi asara da jin zafi kafin kawo karshen wasu kamuran, to me zai hana Gwamnati ta tayi nazari, tare da zama na musamman dasu ASUU din dan kawo karshen lamarin tin kafin wuta ya kunno kai.


Ana gab da siyasa ta 2023, wasu na iya anfani da wannan yajin aikin dan yin kampen. Idan har wasu yan siyasa zasu iya yakar baka tare da furta karerayi dan ganin sunyi nasarar lashe zabe, ina kuma ga batun yajin aiki. Da yawa daga cikin yan siyasa na iya anfani da wannan yajin aikin dan su yake abokiyar hamayyar su.


Muna rokon Allah ya kawo mana zaman lafiya, ya bamu ilimi mai albarka, ya bawa kasar mu albarka, ya taymaki yan kasar mu. Ameen ya Allah.