Alamace ta haduwa
Wannan alama ce da take nuna ce wa zamu hadu a nan gaba
A daren farko na watan Ramadan, farkon wanda ya fara kawo min ziyara abokina Aliyu Asadullah Alincy.
Duk da cewa baya nan a raye, amman maganar gaskiya ruhin sa na tare damu. Tabbas haka ne, kafin na kwanta jiya nayi tunanin waye zan kira daga abokai na dan taya su murna da shigowa wannan watan. Na kira wasu da rana, da dare kuma sai naji wani irin kasa da gajiya, duk da cewa ina son nayi kiran dan ziyara, amman baiyu ba.
Bayan da bacci ya dauke ni, kawai sai gaji Abokina amini na, ya kawo min ziyara ta musamman. Na kalle shi a yanayin da naji a raina kamar yana nan bai rasu ba. Ni har tambayar sa nayi, tin da kana iya zuwa har gida mai zai hana ka dawo baki daya, dan gaskiya ina bukatar ka abokina. Kawai yayi min murshi, sannan yace "aikuwa".
Yanayin ya nuna, gamu a cikin gidan su, da baban shi da kuma kannen shi, har da su umma a mafarkin.
Ba sai nayi doguwar bahani ba, domin ba dole bane na kawo tattaunawa da mukayi gaba daya ba. Domin shi mafarki watarana yana zuwa ne a gaske, wani lokaci kuma abinda mutum yafi tunani akai, ko abinda yafi rikewa a rai, to hakikanin gaskia zai iya zuwa masa a mafarki.
Duk da cewa, mafi yawan mafarkai na suna faruwa da gaske bayan aukuwan shi. Kashi 60 na iya zama gaskia, Kashi 20 bana bukatar ya zama zahiri, duk da cewa ba mai iya kauce ma kaddara ta Ubangiji. Sauran kashi 29 din kuma karya ne domin ba zai ma taba yiwu ba.
Koma menene, wannan yana alamta cewa gaskia zamu hadu da abokina Alincy. Sannan hakan na iya zama daga cikin farkon mutanen da zasu tarbe ni a farkon Isa ta na tafiya da zanyi Insha Allah.
Allah kasa shahidan abokai na su tarbe ni a gobe kiyama. Kasa kar mu wulakanta saboda su. Allah ya sanya Alkhairi, ya sa muna daga cikin wayanda karshen su mutuwar shahada zasuyi. Allah shahafa mafi daraja da daukaka. Allah zunuban mu nake roko ka goge mana. Allah ibadaun mu na jiya da na yau da na gobe nake son ka karba mana. Allah abokina nake son ka daukaka shi. Allah iyayen mu da suke can ka dube su. Allah ka gafartawa kakannin mu da suka rigamu tafiya. Allah ka daukaka darajar mu a duniya da lahira, ka jikan mu, ka yalwata zukatan mu, ka bamu arzikin duniya da lahira. Allah badan mu ba, face alfarmar shaheedan ka da suka riga mu zuwa gidan gaskia.
Ameen ya Allah
Ameen ya Allah
Ameen ya Allah