Wanene Aliyu Asadullah? Shashi na 1 Babi na 1
*Sashi na (1): Waye ne Aliyu Asadullah?
Babi na (1)
* Cikakken rahoton renakun haihuwar sa.
I.. ...Rana da aka haife shi.
II..... Kwankin watan haihuwar sa.
III.... Zuwan sa duniya da kuma murna da mama da baba sukayi.
1.1.1Sunan shi Aliyu, an haife shi a ranar Litinin, da Subahi misalin karfe 4:00am na safe, a watan Zulkeedah 29/11/1417, dai-dai 22 ga watan Ogusta 01/10/1997. Maman da baban shi sunyi farin ciki sosai da zuwansa, ganin cewa shine da na farko a wajen su. Sannan ya samu gata da kulawa daga garesu.
2.Wane irin karanci yazo dashi?
I.... Baiwa da kuma yanayi lokacin da yake jinjiri.
II.... Tin Yana karami, yana tare da mutane
III.. Farkon abinda ya fara koya da kuma wurin da ya fara koyo
1.1.2 Aliyu shi ya kasance me karama, Saboda ya samu karramawa tun daga wajen kakan su daga bangaren Mahaifi da kuma mahaifiya. Ganin cewa shine jikansu namiji na farko. Shdin ya kasance jika na farko daga ko wanne bangare na iyayen mahaifan sa. Shi din Allah ya masa baiwa tun yana jariri. Daga cikin baiwar sa na jarirantaka akwai yawan kuka, saboda duk yaron da yakasan ce mai yawan kuka yakan zama yaro ne mai tausayi sosai. Hakan ya tabbata saboda kuwa yana da tausayi sosai. Sannan baiwar karatu dan ko acikin aji yakan zama haziki. Shi din yaro ne mai son mutum, tun yana karami yakasan ce yaro ne wanda baida kiwuya, ma'ana yaro mai son kowa, sannan kuma yana da saurin sabo da mutane musamman ga yan’uwan sa. Ga iya wasa da mutane, duk yana daga cikin halayyar sa da zai sa yaro yaza ma yana da mutane. Ya koyi abubuwa daban-daban awajan iayeyen sa. Musamman Ibadu kamar su; Sallah, Azumin Litinin da Alhamis. Ya kasance tun bai kai shekara bakwai (7) ba yake son yin Azumi, har ya kan ce wa mama nima zanyi Azumin goben, saboda ya gane cewa Litinin da Alhamis anayin Azumi. Tin mama tana hana shi, sai mahaifinsa yace kibar shi ya saba tunda yana sonyi.
3. Dalilin da yasa aka sa masa suna Ali
I.... Shin Umma taso a sa masa suna Ali
II... Cikakken bayani game da sunan shi Ali
III...: Shin yana da zuciya irin na Ali ?
1.1.3 Sunan shi Ali, kamar yadda muka sani, an sa masa suna Ali ne , saboda an haife shi a watan da aka haifi Imam Ali Arridah, daya daga cikin jerin jikokin Manzon Allah (SAW). Da yake a baya idan aka haifi yaro a kanje gaban magabata a tambayi su wane suna za a sa masa. Malam Mustapha Lawan Nasidi shi aka tambaya akan wane suna ya kamata a sa masa, sai Malam Mustapha yabce "a sa masa suna Ali. Saboda a wannan watan aka haifi Imam Ali Arridah", waton watan Sulkidah kenan. Ali yasamu nasaba ne daga wajen Imam Ali Haidar, wato kanin manzon Allah (s.a.w) shi kuma sakamakon cewa wannan watan bashi ne watan haifuwar Umam Ali Haidar ba kuma ba Gadeer ba shiyasa, amma Duk Ali ne kawai kowanne Ali yanada lakabinsa. Ya kasance shima kamar sauran Ali, yana da zuciya, kusan za a iya cewa zuciyar tama Fu sauran Alin.
4. Halayyar sa na yarantaka
I...: Dabi'un sa na Yarantaka
II...: Dabi'un sa da suke burge iyayen sa
III...: Dabi'ar da mutane kafin ya fara zuwa makaranta.
1.1.4 ya kasance mutum mai halaye kyawawa, wanda kusan kowa yana yabawa da irin kyawun halin sa. A halayyar sa na yarantaka gaskiya yasha ban- ban da sauran wasu yaran, duk dama shine farko awajen mama amman shidin na musamman ne gaskiya, duba ga yanayin yadda dabi’un sa yake. A lokacin da yana karami ya na da dabi’ar tambaya, yakan yi tambayoyi akan abubuwa daban-daban, dan kuwa shi din yaro ne me yawan tambaya, har idan mahaifinsa zai fita sai ya ce Baba ina zaka je ?, Sai ya ce Baba nima zanje, yayi ta tambaya har mahaifin sa yake cewa “anya kuwa yaron nan ba Dan Jarida zai zama ba” saboda tambaya irin nasa. Akwai abubuwan burgewa sosai dangane da yaran takarsa, musamman ma wargi saboda shi ya kasance mai kazar-kazar, yakan yi komai da izza, kuma a gurguje ba bata lokaci, saboda ko aike ne akayi masa yanzu zaije ya dawo da wuri kuma bazai tsaya wasa ba, wannan ma yana burge su mama da baban su sosai. Har ila yau, mutane da yawa sukan yabi halayan sa, saboda shi tin yana karami yake kula da kannen sa, ko idan an tashi daga makaranta zai kama hannun kaninsa su tafi gida tare. Sannan yana kiyaye lokutan tafiya makaranta sannan baya karya dokar makaranta duk tsanani.
5. Farin jinin sa
I....: Yadda mutane ke ji dashi a lokacin da yana dan Yaro
II...: Irin nishadi da farincikin da yake sa su umma da Abba
III...: Karin bayani daga haihuwar sa har zuwa lokacin fara zuwa makaranta
1.1.5 Ali ya kasance mai farin jinin jama’a, kama da ga yan’uwan sa na jini da yan’uwa sa na Addini da kuma sauran mutane gaba daya. Hakazalika suma Iyayen sa suna ji dashi sosai, kasan tuwar sa na zama shine Da na farko, sannan kuma shine babban jika namiji a wurin ka kaninsa. Shi ya kasance mutum ne me ban dariya, yakanyi abu dan yaga farin ciki a fuskar kowa, sannan yakan guje duk wani abin da zai bata ma kowa rai. An haife shi ranar Litinin kamar yadda ya gabata a farkon babi. Kuma an yi farin ciki sosai da haifuwar sa, sannan Allah yayi shine yana son makaranta sosai, dan kuwa tin kafin asashi makaranta idan yaga yaran gidan su zasu tafi har yakan bisu ma makarantar. Har shima aka kaishi malamai suka ce yayi karami, amma a hakan bai daina zuwa ba har malaman suka hakura suka karbeshi.
Atakaice: An haife shi ranar Litinin da Asubah misalin karfe Hudu. Saukan asubabi, kuka rana mai albarka. Yazo duniya 29 ga watan Zulkada 1417, dai dai 22 ga watan 8 1997. An haife shi a karshen karni na 19. Mutum ne Mai son karatu, saboda tin yana yaro yake bin yara zuwa makaranta. Baya son bacin ran mutane, kuma yana da son wasa dan mutane suyu farin ciki. Yana son kannen sa, dan ko an tashi makaranta sai ya jira sun tafi gida tare. Haka zalika shi din mutum ne mai yawan kuka lokacin da yana yaro karami, hakan yana sa mutum ya zama mai tausayi kuma hakan ya faru dashi. Ya samu suna Ali ne saboda an haihe shi a watan da aka haifi Ali Arridah. Shidin kamar saurin Ali ne, yana da zuciya. Kuma mutum ne mai yin komai da izza, domin akwai shi wargi da kuma kazar-kazar wanda ko aike aka masa zai dawo nan take kamar kamar ka aike Mikiya.
Tags:
Alincy Library
